An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, ta kama wani direban mota ɗauke da jabun kuɗi har Naira miliyan ɗaya.

Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar cewa jami’an sintiri na Gwamnatin Tarayya ne suka tsayar da direban a kusa da gidan Guru Maharaji, kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Direban mai suna Akande, ya fito daga Legas ne, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Osogbo, babban birnin Jihar Osun, kafin shiga hannu a ranar Juma’a.

A cewar Osifeso, lokacin da aka tsayar da motar, direban ya fara rawar jiki abin da ya sa jami’an suka binciki motarsa, inda suka gano kuɗin a cikin wata leda.

Mota da yake tafiya da ita ƙirar Toyota Sienna ce mai lambar FKJ 443 YG.

Akande, ya amsa cewa wani mutum ne ya ba shi kayan a garejin Ojota, Legas, inda aka ce man shafawa ne da za a kai Osogbo.

Amma da aka bincika, aka gano duk jabun sabbin kuɗaɗe ne masu lambobi 235923, 235922, da 235921.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *