Duk ɗan APC ya tsira daga tuhumar cin hanci — El-Rufai
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce dole ne a kawar da tunanin cewa mambobin jam’iyyar APC sun tsira daga zargin cin hanci da rashawa.
Ya jaddada cewa dole ne a riƙa bincikar kowa ba tare da nuna bambanci ba.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a jawabinsa a taron muhawarar Daily Trust karo na 23, wanda aka gudanar a Abuja, ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Sakkwato
- EFCC ta ƙwace kadarorin Malami na Naira biliyan 213
Taron, mai taken “Jamhuriya ta Huɗu ta Nijeriya: Me ke aiki, kuma mene ne ba ya aiki?”, ya mayar da hankali ne kan halin da dimokuradiyyar ƙasar ke ciki.
A cewarsa, adalci, gaskiya da shugabanci nagari su ne ginshiƙan samar da ingantaccen mulki a Nijeriya.
Ya ce, “Ana tafiyar da mulki ba tare da bin ƙa’ida ba. A Najeriya, an fi yin garambawul da sakaci a harkokin mulki fiye da yadda ake gudanar da zaɓe.
“Muna shirya zaɓuka, muna kafa hukumomi, muna sanar da kwato kadarori, amma a aikace, daftarin mulki yana ci gaba da kasancewa abin da ake jingina da shi ne kawai.”
El-Rufai ya ƙara da cewa, a wasu lokuta ana amfani da zargin cin hanci da rashawa ne a matsayin makami kan ’yan adawa, yayin da wasu ke tsallakawa zuwa APC ba tare da fuskantar tuhuma ba.
Ya ce, “Cin hanci da rashawa ya zama barazana ga wasu, yayin da ake yin sassauci ga wasu da ke shirin shiga APC. Ba a zargin mambobin APC da laifin cin hanci da rashawa. Wannan ba magana ba ce kawai; ana ganinsa a albashin da ba a biya ba, ayyukan da aka yi watsi da su, da lalacewar ababen more rayuwa.”
Ya jaddada cewa idan ba a aiwatar da doka yadda ya kamata ba, halaye marasa kyau sukan yawaita ba tare da hukunci ba, wanda a ƙarshe ke jefa ƙasa cikin ruɗani.
Dangane da hanyoyin magance matsalar, El-Rufai ya ce dole ne Nijeriya ta ƙarfafa hukumominta ta hanyar yin garambawul a bangaren shari’a, domin tabbatar da sahihin zaɓe da kuma ’yancin hukumar zaɓe mai zaman kanta.
Ya ce, “A ƙarshe, dole ne mu dawo da gwamnati mai ɗa’a, domin siyasar mu ta zama mai ma’ana. Sauyi ba wai kawai abin da ya kamata a canza ba ne, har ma da abin da ya kamata a daina.”
A taron, an kuma saurari jawabai daga Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Sunday Dare, da kuma tsohuwar shugabar kwamitin kula da harkokin ƙasashen waje a Majalisar Wakilai ta 7 da ta 8, Honarabul Nnenna Elendu-Ukeje.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, shi ne ya jagoranci taron, yayin da Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, ya halarci taron a matsayin babban baƙo na musamman.
[ad_2]
Source link