Sin Na Adawa Da Lalata Tsarin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Duniya Bisa Kafa “Karamin Rukuni”
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya ce kiyaye yanayin kasuwanci mai bude kofa ga duniya da samun moriya ga kowa tsakanin kasa da kasa, ya dace da muradun kasashen duniya, kuma Sin na adawa da wata kasa ta lalata tsarin tattalin arziki da cinikayya na duniya bisa kafa wani “karamin rukuni”.
Guo Jiakun ya bayyana haka ne a yau Jumma’a, yayin taron manema labarai na yau da kullaum, lokacin da ya ke amsa tambaya game da matakan da suka shafi batun “ma’adinai masu muhimmanci” da Amurka da Japan da sauran kasashe suka dauka.
Game da hare-haren da aka kai wa wata makarantar firamare dake Iran, Guo ya ce, bangaren Sin ya yi ta’azziyar daliban da suka rasu a hare-haren, kuma kungiyar agaji ta Red Cross ta Sin ta yanke shawarar ba da agajin gagawa na dalar Amurka dubu 200 ga kungiyar Red Cross ta Iran, don taimakawa iyayen daliban da suka mutu.
Bugu da kari, game da shirin raya kasa na Sin na shekaru biyar masu zuwa, Guo ya ce, Sin za ta dage wajen zama karfi mai muhimmanci, da daidato, da kuma adalci a duniya.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link