Gwamnatin Trump ta caccaki CNN kan rahotannin yaƙin Iran
[ad_1]
Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta caccaki kafar yaɗa labarai ta CNN kan yadda take kawo rahotanni dangane da yaƙin da ƙasar ke fafatawa da Iran, lamarin da ke ƙara buɗe sabon babi a rikici tsakanin Fadar White House da kafafen yaɗa labarai.
Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya yi kakkausar suka kan wani rahoton CNN da ya ce Washington ba ta yi tsammanin Iran tana da ƙarfin kawo cikas a zirga-zirgar man fetur a Mashigar Hormuz ba.
Hegseth ya bayyana rahoton a matsayin wanda “ba shi da tushe”, yana mai cewa yana fatan shugaban kamfanin Paramount Skydance, David Ellison, zai kammala saye kafar domin samun abin da ya kira “kafofin watsa labarai masu kishin ƙasa”.
Kamfanin Paramount Skydance na shirin karɓe ikon kamfanin Warner Bros. Discovery, wanda a halin yanzu shi ne mai CNN, bayan ya sha gaban Netflix a takarar sayen kamfanin.
A nata ɓangaren, kakakin Fadar White House Karoline Leavitt ta ce rahoton CNN game da yiwuwar rufe Mashigar Hormuz “ƙarya ce ɗari bisa ɗari”, tana mai cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka ta daɗe tana shirya wa irin wannan barazana.
Sai dai shugaban CNN Mark Thompson ya mayar da martani da cewa tashar za ta ci gaba da faɗar gaskiya ga masu kallonta, duk da matsin lamba ko suka daga ɓangaren ’yan siyasa.
Rikicin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da kai hare-haren soja kan Iran a wani farmaki da ake kira Operation Epic Fury, wanda ya ƙara dagula rikicin a Gabas ta Tsakiya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link