Shugabar ALGON Ta Kano Ta Buƙaci Dakatar Da Aiyukan Siyasar Ado Doguwa

[ad_1]

Shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar ƙananan hukumomi ta Nijeriya reshen jihar Kano Saadatu Salisu Soja Maijama’a, ta buƙaci vGwamnatin Tarayya da ta jihar da su shiga lamarin mutuwar wani mazaunin yankin da ta faru yayin wani shirin tallafi.

Lamarin ya faru ne a wani shirin rabon kayan taimako da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya shirya. Ta bayyana cewa wanda ya rasu shi ne Buhari Mai Fulawa, wanda ta ce ɗaya ne daga cikin ‘ya’yan Tudun Wada.

  • && Kano && Amince Da Ayyuka Na Sama Da Biliyan ₦310
  • ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

A sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Juma’a, Soja Maijama’a ta bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar yankin, tana mai addu’ar Allah Ya ji ƙansa da rahama tare da bai wa iyalansa da al’ummar Tudun Wada juriyar wannan rashi.

Ta kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da ɗaukar matakan da suka dace. A cewarta, ya kamata a dakatar da Hon. Ado Doguwa daga duk wasu harkokin siyasa da taruka har sai an kammala binciken da ake yi kan lamarin.

Wannan kira na zuwa ne yayin da ake nuna damuwa kan tsaron jama’a a lokutan tarukan siyasa da shirye-shiryen al’umma. A baya-bayan nan, Doguwa tare da shugaban ƙaramar Doguwa, Abdulrashid Rilwan, sun raba kayan abinci da kuɗaɗe ga mazauna yankin. Haka kuma a shekarar 2023 an gurfanar da Doguwa a kotu kan zargin haddasa tashin hankali yayin zaɓe, amma kotu ta wanke shi a shekarar 2024.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *