An kashe sojoji biyu yayin rikicin matasa a Kuros Riba
[ad_1]
Wasu sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin raba rikicin da ya ɓarke tsakanin matasan ƙauyukan Isabang da Alesi da ke Ƙaramar Hukumar Obubra a Jihar Kuros Riba.
Rahotanni sun ce rikicin ya faru ne a ranar Asabar, bayan wata takaddama da ta fara tun makon da ya gabata tsakanin matasan ƙauyukan biyu.
An ce lamarin ya samo asali ne bayan da wasu matasa suka lakaɗa wa wani mutum mai suna Ibrahim Musa duka a wani wurin binciken ababen hawa da jami’an tsaro ke aiki.
Wani jami’in tsaro mai suna Joshua Erin ya sanar da sojojin Bataliya ta 245 da ke barikin Ejor game da rikicin, inda aka tura sojoji domin kwantar da tarzomar.
Sai dai yayin ƙoƙarin da suke yi na sasanta rikicin, matasan da ke faɗa suka kai hari kan sojojin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyun nan take.
Mutuwar sojojin ta haddasa tashin hankali a yankin, inda aka ce wasu sojoji sun mayar da martani, abin da ya janyo ƙarin asarar rayuka da jikkatar wasu.
Rahotanni sun ce wasu matasa biyu — Christopher Agara da Ogobi Egbe — sun mutu a artabun, yayin da wasu da dama suka jikkata aka kai su asibiti domin samun kulawa.
Lamarin ya tilasta wasu mazauna yankin tserewa daga gidajensu domin fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo.
Sai dai rahotanni sun ce zuwa yanzu hankula sun fara kwanciya, yayin da al’ummar yankin suka koma gudanar da harkokinsu bayan lafawar rikicin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link