Mece Ce Soyayyar Annabi SAW?
[ad_1]
Assslamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Wa radiyallahu an ashabi Rasulullahi SAW, wala haula wala kuwwata illa billahil aliyul azim.
Mun gode Allah da ya sake hadamu a wannan gida na freedom radio Mai albarka wanda ya ke wayar da kan al’umma da al’amuran yau da kullum,
- Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
- Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
Mun gode Allah, wannan lokaci ya yi daidai da lokacin murnar haihuwar manzon Allah SAW, wanda yazo da wani sabon salo mai dadi na murnar cikarsa shekara 1,500 da haihuwa. Duk wanda ya kai shekara 30 a duniya yaga murnar cikar haihuwar Annabi Isa AS shekara 2,000 wanda duniya gaba daya ta yi murna
Mun gode Allah, haka yanzu duk musulmai da duniya suna murna da cikar Annabi SAW 1500 da haihuwa.
Don haka, duk wanda Allah SWT ya nuna masa ganin wannan lokaci, abun ya yi wa Allah godiya ne da ya nuna masa wannan lokaci. Wasu daga magabata, sun yi murna da suka ga cikar Annabi SAW shekara 100, wasu sun yi, a shekara 500, wasu sun yi a shekara 1000 mukuma ga shi mun ga cikar haihuwar Annabi SAW shekara 1500.
Ana cewa, sai kasan abu, sannan zaka san waye shi har kaso shi. Allah SWT ya yi ma Annabi SAW ni’ama da yawa, domin ya zabe shi cikamakon Annabawa, duk Annabawa Allah da ma’aika sai Allah ya zabesu ta bangaren cikar halitta, sai kaji ance mai kyau ne, mai dadin murya ne, mai Amana ne, mai farin jini ne, kuma mai hankali.
Gaskiya, Hankali, da Amana su ne abubuwa 3 da duk DanAsam sai ya zama yana da su, ta yadda zai zama yana tunani sama da na jama’a.
Allah yana karrama wasu da cikar jiki, ya zama dogo (mai matsakaicin tsawo), mai dadin murya sabida isar da sako, sabida ana cewa, “idan mutum yana da dadin murya, malamin wani ne, amma akasin haka, malamin kansa ne.” Idan mutum yana da dadin murya, in yana karatu ko waka, za ka samu da yawan mutane suna son saurara. ya’isa gane dadin murya Allah SWT yace, “mafi kin sauti, shi ne sautin jaki, a dadin murya kuwa, Doki mai haniniya”, inda wasu suka ce wai in akaji doki ya yi kuka wai yaga Mala’ika ne shi kuwa jaki, in ya yi kuka, wai yaga Aljani ne.
Sayyadina Umar (RA), duk in yaga Abu Musal Ash’ari, sai yace, tuna mana Ubangijinmu, sabida dadin muryarsa, sabida haka, murya tana daga cikar Annabawa, haka Annabinmu SAW mai dadin murya ne kuma shi ne ya tattara kyawawan dabi’u na duk Annabawan Allah.
Bayan ni’imomi da ya yi masa na cikamakon wannan addini da littafi da ilimi, Allah ya turo Annabi SAW don ya ceto mu a yayin da muke daf da fadawa wuta. Kaga yanzu ya zama dole mu rungumi Annabi SAW da soyayya, tunda mutum yana son wanda ya yi masa alheri.
To ita Soyayya an rabata kaso hudu 4 ko biyar 5:
Akwai ta ibada wadda In ka yi ta, za ka samu Lada kuma ka cika mutum, in ba ka yi ta ba, kana da zunubi. Ma’ana ya zama dole duk Dan’Adam ya yi ta, haka Allah yake nufin ‘yan Adam da ita, sai dai, tawani tafi tawani, yanzu duk garin da kaje, duk wayewa da cigaba na wannan wurin, sai kaga dakin bauta, inda dan Adam zai ji cewa, yanzu ya zo, wurin ubangijinsa, koda icce ne suka sassaka ko mutum-mutumi ne. Kafin ka raba mutane da irin wannan soyayyar ta ibada, sai an sha wahala sosai. Kaga wannan soyayyar ibada ce da Allah yasata a cikin duk ‘yan Adam. A irin wannan soyayyar ce, sai Allah ya aiko wa ‘yan Adam Annabi, yace musu, nagode Amma ga yadda za a bauta min.
To wannan itace soyayyar Allah, shi yake fara sonmu sai muso shi, “Yuhibbuhum wa yuhubbunah”, yana daga hadisin Annabi SAW wanda duk sufaye suka rikeshi hannu bibbiyu, Allah yace, “Nakasance taska da ba a sannin ba, sai naso a sanni, sai na halicci wata halitta wacce da ita aka sanni”, sai sufaye suka gane cewa, Allah ya hallici halitta ne don yana sonta, ba dan ya konata ba. Za kaga duk halitta tana son Allah, batun aikata laifi kuma daban yake da bangaren soyayya. za kaga mutum yana laifi amma luma yana kuka, wani ma har ya kai kansa da kansa gaban hukuma domin a ladabtar da shi domin yana son Allah. Duk an ga hakan a zamanin Annabi SAW. Wani mutum yana shan giya kuma abun yana damun shi, sai ya zo gun Annabi SAW don ya yi masa nasiha amma duk da haka, ya kasa daina wa, har wata rana Annabi SAW ya dauki takalmi yana dukansa, inda wasu sahabbai dake wurin suka taya Annabi SAW, sayyadina Umar, shi kuma sai ya hada da zagi da la’anta, nan take Annabi SAW yace, a’a Umar, yana son Allah, yana son Annabinsa. Tanan malamai suka gane cewa, mutum ko yana sabo, zai iya zama masoyin Allah.
Sabida haka, Sayyadina Ali ke cewa, Shaidan baya zuwa wurin Wanda baya son Allah, haka Barawo, baya zuwa gida sai gidan wanda yake da abun da yake bukata, “mai son Allah, shi ne zai saba masa sannan ya dawo ya tuba.”
Yazo a hadisil kudusi, Shaidan zai je wurin Allah yace, “Allah bayinka suna sonka amma kuma suna saba maka, ni kuma, suna kina amma kuma suna bina” sai Ubangigi yace, “narantse sai na yafe musu sabon da suka yi mini sabida suna sona, kuma sai na yafe musu binka da suka yi sabida suna kinka”, sun bika ne sabida abin rudi da ka nuna musu, ba don suna sonka ba, ni kuma ba sun saba mini bane sabida suna kina.
Magana akan soyayyar Allah, magana ce mai girma har yazo a hadisi cewa, “fiyayyun bayin Allah, sune wadanda suke nunawa mutane son Allah da rahmarsa ba masu tsoratar da su ba, har mutum yaji ni meyasa ma aka halicce ni”.
Son Manzon Allah SAW dole ne. Allah ne ya sanya mana soyayyar, sai dai tawani tafi tawani, za kaga wani sabida ya hada da bi ko ibada, yana yinta cikin sauki sabida soyayyar, wannan itace soyayyar wajibi, to yanzu kowa shi yasan irin dabarar da zai yi don soyayyarsa ta karu.
Yazo a hadisi cewa, “Abubakar bai fiku ba, sai da Soyayyar Allah da ta Manzonsa,” sai son littafin Allah da son malamai wadanda za su nuna maka yadda zaka yi bautar Allah da rahmarsa. Magadan Manzon Allah a na’ibance suma sun shiga cikin wannan.
Na biyu daga cikin rabe-raben soyayya, itace soyayyar girmawa: wannan irin soyayya, itace ta son iyaye da girmamasu da kyautatawa da sonsu da yi musu biyayya ta inda bai saba wa Allah ba, bai hadu da son rai ko ziga ba, in ta hadu da wannan, ba za a yi musu biyayya ba, saidai a girmamasu.
Na uku, son shuwagabanni wadanda za su kiyaye mu, musanman masu damara kamar Soja, Dansanda, da dai sauransu. Duk mai son kasa ta cigaba sai ya so su, ya yi musu biyayya. Dole ne mutum yaso shugabanni kuma ya yi musu biyayya yadda tadace.
Na hudu, So na tausai, kamar ‘ya’yan da muka haifa, son da muke musu ba irin wanda muke yi wa iyayen mu ba ne, so ne na tausayi, zamu sasu a makaranta don a koya musu rayuwa ta addini da ta duniya. Shi son girmamawa, karami ne ke yi wa babba, shi kuma son tausayi, babba ne ke yi wa karami.
Na biyar, so na sha’awa, shi ne wanda muke yi wa matanmu, ba irin wanda muke yi wa mahaifiyarmu ko kannenmu ba, sai son mota da sha’war kaya masu kyau yazo a hadisi, “Allah mai kyau ne, yana son mai kyau”.
To shi son Manzon Allah, so ne na ibada da wajibi ba na sha’awa ba ko ganin dama ba.
[ad_2]
Source link