’Yan arewa mazauna Legas na neman taimako kan rusau ɗin Mile 12

[ad_1]



Shugaban Kungiyar Al’ummar Arewacin Najeriya mazauna jihar Legas, Alhaji Abdullahi A.A Fulani ya yi kira ga gwamnati da manyan Arewa da su tallafa musu kan rusau din da gwamnatin jihar Legas ta yi wa gidajensu sama da 5,000 a kwanakin baya.

Ya bukaci kafafen yada labarai, ma’aikatun shari’a da masu hannu da shuni da su duba halin da al’ummarsa suka tsinci kansu.

A makon da ya gabata ne rushe-rushen da gwamnatin Jihar Legas ta gudanar a unguwar Mile 12 ya jefa dubban mazauna unguwar cikin halin kunci, musamman ’yan Arewacin Najeriya da ke zaune a can.

A zantarwarsa da Aminiya, shugaban ya ce rusau din ya jefa su cikin halin kaka-ni-ka-yi, kuma suna bukatar dauki.

Ya ce, “Hakika mun shiga jarabawar zalunci da nuna wariya. An rushe mana tattalin arzikin da muke dogaro da shi wajen rayuwar mu da ta ’ya’yanmu a lokaci guda.”

Shugaban ya ƙara da cewa lamarin ya jawo dubban iyalai rasa matsuguni da abinci, inda ya ce yanzu wasu a kan titi suke kwana saboda ba su da wurin da za su je.

Ya roƙi al’ummar da su taya su ci gaba da addu’a da neman taimakon Ubangiji a cikin wannan lokacin mai cike da ƙalubale.

Alhaji Abdullahi ya ce bayanan da suka tattara sun nuna sama da gidaje, masallatai da makarantun Islamiyya 5,000 aka rushe, abin da ya tilasta sama da mutum 10,000 kwana a kan titi tare da kayansu, ba tare da matsuguni ba.

Mazauna unguwar dai sun koka kan yadda aka ruguza gidaje, makarantu da wuraren kasuwanci ba tare da bayar da isasshen gargadi ba, lamarin da ya jawo koke-koke da zargin nuna wariya da bambanci.

Wasu sun ce rushewar ya rusa tattalin arzikin da suke dogaro da shi wajen rayuwar iyalansu, abin da ya jawo rashin abinci, ilimi da wurin zama.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *