An Shirya Bikin Share Fage Na Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin A Belgrade

[ad_1]

A ranar 4 ga watan Fabrairu bisa agogon wurin, an gudanar da bikin share fage na shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin mai taken “Duniya tana kallon shirin na CMG tare” a Belgrade na Serbia.

An shirya bikin ne bisa hadin gwiwar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG), da ma’aikatar al’adu ta kasar Serbia da kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Serbia da dai sauransu. Shugabar Majalisar Dokokin Serbia, Ana Brnabic ta halarci taron. Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al’umma na kwamitin tsakiya na JKS, kuma babban daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

A cikin jawabinsa, Shen ya ce an riga an gudanar da shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a cikin shekaru 43 da suka gabata a jere, wanda ya bude wata kafa ga masu kallo na duniya don fahimtar kyakkyawan al’adun gargajiyar kasar Sin da ma yadda kasar take a sabon zamanin da muke ciki.

An mayar da taken “Ba za a iya tsayar da gudun dawaki ba” a matsayin babban jigon shirin na bana, inda za a yi amfani da sabbin fasahohin “5G+4K/8K+AI”, da fifikon da CMG yake da shi na yada shirye-shirye da harsuna 85, don samar da wani gaggarumin bikin al’adu ga masu kallo na cikin gida da waje. A cewarsa, shekarar da muke ciki shekara ce ta soma gudanar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, don haka bari mu yi lale marhabin da wani lokacin bazara mai cike da fatan alheri.

Hakazalika, jiya Alhamis, karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Auckland ya shirya liyafar murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar ta Sin, inda aka haska fim na yayata shirin murnar Bikin Bazara wato bikin murnar sabuwar shekarar doki ta kasar, da babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) zai gabatar.

Mahalarta sun nuna cewa, Bikin Bazara na kasar Sin na kara samun karbuwa da jawo hankulan kasashen waje, wanda ya samar da fatan alheri ga kasa da kasa a wannan kyakkyawan lokaci.

Fim din na yayata shirin murnar Bikin Bazara ba wai kawai ya tada tsimin tunanin jin dadi na Sinawa game da bikin bazara ba ne, har ma ya taka rawar da ta dace wajen hada kan wayewar kai daban daban.

Shirin murnar sabuwar shekara na bana dake cike da fatan bil-Adama na hadin kai, zai ci gaba da raka masu kallo na duk duniya don jin dadin wannan gagarumin bikin Sinawa, inda wannan al’ada ta kasar Sin za ta ketare duwatsu da tekuna, da kuma kara samun sabon kuzari bayan dogon lokaci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *