Cutar Sikila Ba Mutuwa Ba Ce
[ad_1]
Ƙwararru a harkar kiwon lafiya sun bayyana cewa, cutar Sikila ko kadan ba tana nuna alamun mutuwa ba ce. Sun bayyana hakan ne, a wani taro da aka gudanar a Abuja; wanda ake kokarin sauya tunanin mutane a kan wannan cuta tare kuma da yin bikin ranar Sikila ta duniya.
Kungiyar ‘Mirror Me’ tare da hadin gwiwar ‘Gehenesphere’ ne suka shirya taron, wanda ya bayar da haske a kan makomar Kobiro Es- elemo, fitacce kuma jigo a cikin al’ummar da ke dauke da wannan cuta ta Sikila.
Babban jami’i na kungiyar ta ‘Mir- ror Me’ da mashiryin taron, Daniel Ojo, sun jaddada bukatar canzawar tunanin al’umma dangane da wannan cuta ta Sikila.
“Cutar Sikila, ko kadan ba ta daukar hukuncin kisa ko wani abu mai kama da haka”, kamar yadda Ojo ya bayyana. Haka zalika, wajibi ne, mu daina kallon masu dauke da wannan cuta a matsayin raunana ko kasassu a cikin mutane, domin kuwa suna da karfi da kuma juriya irin nasu, sannan lokaci ya yi da al’umma za ta gane tare da fahimtar hakan”, in ji shi.
Olunaike, babban mai jawabi a wajen taron; ta goyi bayan wannan furuci na Ojo, inda ta jaddada muhimmancin nuna halayya mai kyau da kuma bukatar tallafa wa al’ummar da ke dauke da wannan cuta ta Sikila. Sannan, ta bukaci ma’aikatan kiwon lafiya da su kasance masu tausayi da jin kai da tausasawa tare kuma da nuna taka-tsantsan wajen amfani da miyagun kwayoyi a tsakanin marasa lafiya.
“Dole ne mu kawar da tatsuniyar cewa, masu dauke da wannan cuta ta Sikila na shan wahala wajen shan magungunansu, ko shakka babu, wannan kawai wani shaci fadi ne da mutane suka jima suna shata suna fada.
“Sannan, masu daukar ma’aikata, su ma dole ne su cire son zuciya da son rai wajen daukar masu cutar Sikila aiki. Domin kuwa ko shakka babu, wadannan bayin Allah na da dama tare da ‘yanci da kuma kwarewa kamar kowa da kowa a fadin wannan kasa”, in ji Olunaike.
Da yake yin nasa karin hasken, Obye Ewuge kwararren likitan jini a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Keffi ta Jihar Nassarawa, ya jaddada yadda za a magance kamuwa da cutar da kuma kula da masu ita yadda ya dace.
Haka zalika, ya sake Bljaddada muhimmancin neman kulawar likita, lokacin da ake cikin tsanani da tashin hankali; maimakon dogaro da magunguna kadai.
Har ila yau, cutar Sikila ba mutuwa ba ce; domin kuwa masu dauke da cutar, su ma mutane ne kamar kowa da ke da kima, ilimi, hazaka, basira da mutuntaka a tsakanin al’umma, don haka, wajibi ne a mutunta su tare da ba su dukkanin gudunmawar da ta kamata.
[ad_2]
Source link