PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote
[ad_1]
Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas.
Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025.
Da misalin ƙarfe 6 na safe, mambobin ƙungiyar da ke aiki a ɗakunan kula da na’urori suka daina aiki.
Umarnin ya shafi mambobin da ke ofisoshi, kamfanoni, da hukumomin gwamnati a faɗin Najeriya, waɗanda za su daina aiki da misalin ƙarfe 12:01 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Satumba.
Okugbawa, ya ce ba za a yi wani aiki a wuraren da abin ya shafa ba sai dai idan ya shafi tsaron rayuka ko kayan aiki, kuma sai da amincewar babban ofishin ƙungiyar.
Ƙungiyar ta kuma umarci a dakatar da dakon ɗanyen mai da gas zuwa matatar man Dangote.
Ta buƙaci mambobin da ke aiki a manyan kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa (IOCs) su rage yawan dadin gaske da ake kai wa matatar Dangote.
A cikin sanarwarta, PENGASSAN ta nemi mambobinta da su yi addu’a “don Allah ya bai wa shugabanni ƙarfin gwiwa su tilasta Dangote da sauran ’yan kasuwa su girmama dokokin ƙasa.”
Yajin aikin ya biyo bayan korar ma’aikata sama da 800 daga matatar, wanda kamfanin ya tabbatar a ranar Juma’a a matsayin wani ɓangare na sake tsara harkokinsa.
Kamfanin ya ce “’yan kaɗan ne abin ya shafa,” amma ƙungiyar ta ce hakan rashin adalci ne, ta kuma buƙaci a dawo da dukkanin ma’aikatan da aka kora.
A martaninta, matatar Dangote ta zargi PENGASSAN da yunƙurin lalata harkar samar da makamashi a ƙasar na ta hanyar umartar a dakatar da kai mata ɗanyen mai da gas.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link