Illolin Tsarki Da Sabulu Ga Mace (2)
[ad_1]
A gaskiya, wasu daga cikinsu na amfani da hannayensu wajen cusa wadannan magungunan cikin jikinau , abin da ba su sani ba shine, idan su ka dauki tsawon lokaci su na aikata hakan, sai ya haifar mu su da matsewar jikinsu fiye da kima. Mun sha samun matsalolinan.
“Idan mace ta samu kanta cikin wannan matsala, don warkar da ita akwai bukatar a yi ma ta aikin tiyata nau’i daban-daban ko kuma ayi kokarin samar ma ta da wata saban waje. Kafin a samu nasarar hakan kuma dole matar ta zauna a asibiti tsawon watanni ma su yawa.
- Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar
- An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO
“Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga mace don tsaftace jikinta shine ruwa mai tsabta kawai. Idan ta yi amfani da duk wani abu da yake dauke da wani sanadari kamar sabulu ko turare, zai iya kashe kwayoyin halittar da Ubangiji ya halitta mata don jikinta ya zauna lafiya.
Amma yayin da ta lahanta kwayoyin halittar da Ubangiji ya yi mata, sai kwayoyin cuta su samu damar shiga jikinta. A karshe irin wadannan mata za su fara fitar da gurbataccen ruwa, “inji shi.
Ya ci gaba da bai wa mata shawarar cewa, kama ta ya yi su ke wanke jikinsu da ruwa mai tsafta kadai, kuma “kar mata su damu da wani wari da ke fita daga jikinsu saboda wannan warin dabi’ar da Allah Ya halicci wajen ne, matukar ba wari ne na cuta ba, wanda shi kuma warin cuta ya na kasancewa mai yawa ne”.
[ad_2]
Source link