NNPP: A tura min lissafin kuɗin da ake bi na zan biya — Kofa

[ad_1]



Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana mamakinsa game da korarsa daga jam’iyyar NNPP.

Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana korar Kofa kan zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa da kuma rashin biyan kuɗaɗen da ake bin sa.

Ya kuma yi barazanar kai shi kotu idan bai biya kuɗaɗen da ake bin sa ba.

A martaninsa, Kofa, ya ce: “Korata daga NNPP ta zo da mamaki sosai. Ban yi tsammanin tattaunawar da na yi a kafafen yaɗa labarai za ta jawo irin wannan hukunci ba.

“Babu wata gayyata da aka yi min domin na kare kaina, abin da ya saɓa ƙa’ida saboda ba a bai wa mutum dama kare kansa ba.”

Ya ƙara da cewa a shirye yake ya biya bashin kuɗin jam’iyyar ke bin sa ba tare da an je kotu ba.

“Game da batun rashin biyan kuɗina, ina roƙon jam’iyya ta turo min da lissafin kuɗin nan, zan biya nan take. Babu buƙatar hayaniya ko cin mutunci.”

Kofa, ya gode wa NNPP bisa goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikin jam’iyyar, sannan ya gayyaci magoya bayansa da su biyo shi yayin da yake shirin fara sabuwar tafiya a siyasa.

A baya-bayan dai rikicin cikin gida na ci gaba da mamayar NNPP a Jihar Kano, lamarin da ya sanya Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Kawu Sumaila ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *