Shawarar Abinci Ga Masu Ciwon Olsa A Ramadan
[ad_1]
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai zo muku da kalar abincin da mai ciwon Alsa ya kamata yaci:
Idan kina da ciwon Alsa kina shan wahala idan kin dauki Azumi to ga shawara in sha Allah za tayi amfani.
Daga farko dai abinci daya zuwa biyu shine zai kasance abincinki da za ki rinka ci:
- Na farko tuwo ya kasance kin mayar da tuwo abincinki, misali idan ansha ruwa ki samu tuwo kici sosai yadda jikinki bazaiyi nauyi ba.
Bayan nan misalim 12am na dare ki tashi ki kara cin tuwo.
Bayan nan sai da Asuba ki kara cin tuwo, kinga kin mayar da tuwo abincinki a kalla kinci sau 3 ko 4.
2.Idan Allah ya sa kina da hali, kullum ya kasance kina shan Maltina da Madara guda 2 ko 3 ma.
Idan ansha ruwa kisha daya, idan za ki kwanta kisha daya, da Asuba kisha daya.
Ina mai tabbatar miki da cewar in sha Allah idan kika bi wannna matakin za kuyi Azumi ba ta re da kun ta kura kanku ba.
[ad_2]
Source link