NAJERIYA A YAU: Waiwaye Kan Yadda Jam’iyyun Siyasa Suka Kafu A Jamhuriya Ta Hudu
[ad_1]
Ƙarin Podcasts
Jamhuriya ta Huɗu a Najeriya ta fara ne a ranar 29 ga Mayu, 1999, bayan kawo ƙarshen mulkin soja, inda ƙasar ta koma tafarkin dimokuraɗiyya bisa Kundin Tsarin Mulki na 1999. A wannan lokaci ne aka kafa manyan jam’iyyun siyasa kamar PDP, wadda Alex Ekwueme, Solomon Lar da wasu tsofaffin ‘yan siyasa suka jagoranci kafuwarta; APP (daga baya ANPP) ƙarƙashin jagorancin Mahmud Waziri da Abubakar Rimi; da kuma AD, wadda Bola Ige da Abraham Adesanya suka jagoranta, musamman daga yankin Kudu maso Yamma. Wadannan jam’iyyu ne suka kafa tubalin siyasar Najeriya ta zamani, suka buɗe gasa ta ra’ayi, da tsarin zaɓe da ke tafiyar da ƙasar zuwa yau.
Yayin da Jaridar Daily Trust ke shirya taron Daily Trust Dialogue, na wannan shekarar zamu kawo muku jerin shirye shirye mai dauke da taken Jamhuriya Ta Hudu A Najeriya: Abubuwan dake aiki da kuma akasin haka.
A shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zamu yi duba ne kan jam’iyyun siyasa na farko a jamhuriya ta hudu, suwa suka assasa su, da alkawarin da suka yi wa yan Najeriya sai uwa uba shin kwalliya ta biya kudin sabulu daga kafuwarsu zuwa yanzu?
Domin sauke shirn, latsa nan
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link