Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC
[ad_1]
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu.
Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana, tare da wasu jiga-jigai.
Ya bayyaa musu yadda shi da wasu ’yan siyasa wajen kafa jam’iyyar APC a 2013 kuma sun sha wahala kafin kafuwarta.
“Babu wanda zai faɗa min irin wahalar da muka sha wajen kafa APC. Mu ne muka jagoranci kafuwar jam’iyyar, mu ne kuma gwamnoni bakwai na farko da muka ba ta goyon baya.
“An yi amfani da ICPC, EFCC, da ’yan sanda a kaina a wancan lokaci don hana mu cimma burinmu,” in ji shi.
Kwankwaso ya ce duk wata tattaunawa ta haɗin gwiwa ko komawa APC dole ta tabbatar da alfanun da NNPP za ta samu.
“Idan kuna so mu koma APC, dole ku faɗa mana abin da NNPP za ta amfana da shi. Muna da ’yan takarar gwamna a duk jihohi da cikakken tsari a faɗin ƙasar nN. Me za ku ba su idan muka shiga?” ya tambaya.
Ya kuma tunatar da yadda APC da PDP suka saɓa yarjeniyoyin da suka yi a baya.
“Shekaru takwas na APC a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ba su ba mu komai ba, ko godiya ba su mana ba.
“A PDP, abin da muka nema kawai shi ne shugabancin jam’iyyar a yanki guda, amma suka ƙi ba mu. Mun bar su lafiya, kuma yau mun ƙara ƙarfi da ƙima,” in ji shi.
Jagoran na NNPP, ya ƙara da cewa jam’iyyarsa a shirye ta ke don yin tattaunawa, amma ya yi gargaɗin cewa ba za ta yadda a yi amfani da ita sannan a watsar da ita ba.
“Mun shirya shiga APC bisa sharuɗa da cikakkun alƙawura. Ba za mu yadda wani ya yi amfani da mu a jefar da mu ba,” in ji shi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link