Yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ya dagula wa masu zuwa Umrah lissafi

[ad_1]



Rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila ya jefa matafiya Umrah daga Najeriya cikin ruɗani, bayan dakatar da wasu muhimman jirage da kuma rufe wasu sararin samaniyar ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya kawo tsaiko a zirga-zirgar jiragen sama, musamman ta manyan cibiyoyin sauka da tashin jirage kamar Doha da Dubai, lamarin da ya tilasta wa wasu maniyyata ke nazari kan tafiyarsu.

Ƙasashen da suka haɗa da Iran, Iraƙi, Isra’ila, Syria, Kuwait, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, duk sun sanar da rufe wasu sassan sararin samaniyarsu bayan hare-haren da aka kai wa Iran.

Daga cikin kamfanonin jiragen da suka dakatar da zirga-zirga akwai Qatar Airways, Emirates, Turkish Airlines, Air France, British Airways da sauransu.

Sai dai Saudi Arabian Airlines na ci gaba da zirga-zirga, domin Saudiyya ba ta sanar da rufe sararin samaniyarta ba.

Damuwar Matafiya

Wasu daga cikin matafiya sun bayyana fargaba kan tafiyar, inda wani Alhaji Auwal Sani daga Kano da ya maƙale tare da iyalansa, ya ce an soke jirginsa na Qatar Airways, kuma har yanzu ba a ba shi biza ba.

Salihu Shu’aibu ya ce yana tunanin soke tafiyarsa saboda tsoro, yayin da Hajiya Bilkisu ta ce ta ɗage tafiyarta zuwa shekara mai zuwa, tana mai cewa ba za ta yi kasadar tafiya cikin yanayin da ba ta da tabbacin tsaro ba.

Sai dai wani da ke Saudiyya, Hussein Olugbon, ya ce rayuwa na tafiya yadda aka saba a ƙasar, ba tare da wata alamar rikici a biranen Makkah da Madina ba.

Tasirin Rikicin Ga Masu Harkar Umrah

Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Hajji da Umrah ta Najeriya, Alhaji Abdullateef Ekundayo, ya ce dakatar da zirga-zirgar wasu jirage musamman Qatar Airways ta jefa harkar cikin rashin tabbas.

Ya bayyana cewa duk da sararin samaniyar Saudiyya a buɗe yake, manyan tashoshin wucewa kamar Doha da UAE na fuskantar matsala.

Manajan Musab Travelling Agency, Sadiq Musa, ya ce dakatar da jirage ya jefa fasinjoji cikin ruɗani, wasu na neman wasu tafiya ta jiragen Ethiopian Airlines.

Fatima Idris ta Al-Haramayn Travels a Kano ta ce an samu raguwar masu son tafiya, inda kuma kwastomomi da dama ke neman a ɗage musu tafiya ko a maida musu kuɗi.

Shawarar Masana

Masana sun shawarci maniyyata su riƙa bibiyar bayanan kamfanonin jirage da hukumomin Saudiyya da Najeriya kafin su yanke shawara.

Sun ce duk da cewa babu matsalar tsaro a biranen Makkah da Madinah, matsalar dakatar da zirga-zirgar jirage da rufe sararin samaniya na iya haddasa jinkiri ko soke tafiya ba zato ba tsammani.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *