Za a Bude Taro Na Hudu Na NPC Ta 14 Da Safiyar Ranar 5 Ga Maris
[ad_1]
Majalisar wakilan jama’a ta kasar Sin wato NPC a yau 4 ga watan Maris ta gudanar da taron manema labarai a zauren jama’a dake nan birnin Beijing, inda kakakin taron Lou Qinjian ya amsa tambayoyin ‘yan jarida na cikin gida da na kasashen waje game da ajandar taron da kuma batutuwan da suka shafi ayyukan majalisar.
Lou Qinjian ya bayyana cewa, za a bude taro na hudu na NPC ta 14 ta kasar Sin a safiyar gobe 5 ga watan Maris, kuma za a rufe shi da yammacin ranar 12 ga watan Maris. Taron zai dauki tsawon kwanaki 8 ana yi, kuma za a gudanar da manyan tarurruka guda uku. Kazalika, za a gabatar wa babban taron daftarin tsarin “shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15” bayan an tattara ra’ayoyi daga bangarori daban-daban, inda za a yi bincike da zartas da shi, sannan a wallafa da kuma aiwatar da shi.
Bugu da kari, yayin da yake amsa tambayoyin da suka shafi dangantakar Sin da Amurka, Lou Qinjian ya ce, Sin da Amurka ya kamata su mutunta juna, su zauna lafiya tare, da kuma yin hadin gwiwa da cin moriyar juna.
Game da halin da ake ciki a Iran, ya ce, bangaren Sin yana kira da a dakatar da ayyukan soja nan take, da kuma dawo da tattaunawa da shawarwari. Babu wata kasa da ke da ikon sarrafa harkokin kasa da kasa ita kadai, da mallakar makomar wata kasa, da kuma yin yadda ta ga dama da harkokin ci gaba a duniya. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link