Xi Jinping Ya Yi Muhimmin Bayani A Kan Ayyukan Kamfanoni Mallakar Gwamnati

[ad_1]

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a kwanan nan ya yi muhimmin bayani game da ayyukan kamfanoni mallakar gwamnati, inda ya jinjina rawar da suka taka a matsayin ginshiki na aiwatar da manyan tsare-tsare da kuma raya tattalin arziki na kasar.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, a sabon zamanin da ake ciki, kamata ya yi kamfanoni mallakar gwamnati su rike a zuci muhimman ayyukan da aka dora musu, kuma su samar da gudummawarsu a kokarin da ake yi na zamanantar da kasar Sin. Ya bukace su mai da hankali a kan nauyin da aka rataya a wuyansu, kuma su rubanya kokari wajen nazarin muhimman fasahohi da zurfafa gyare-gyare.

Daga ranar 22 zuwa 23 ga wata, an gudanar da taron daraktocin kamfanoni mallakar gwamnati na kasar Sin a birnin Beijing, inda aka isar musu wannan muhimmin umurni na shugaba Xi. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron tare da gabatar da jawabi, kuma daraktocin sassa masu ruwa da tsaki sun halarci taron.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *