Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya bayan ya faɗi a Turkiyya

[ad_1]



Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya bayan tuntuɓen da ya yi har ya kai ga faɗuwa yayin da ya ziyarci Fadar Gwamnatin Turkiyya a wannan Talatar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Suday Dare ya bayyana, yana mai cewa babu wani rauni da shugaban Najeriyar ya samu bayan tuntuɓen.

Sanarwar ta ce tuni shugaban ya ci gaba da ziyarar aiki da ta kai shi Turkiyya, inda tawagarsa ta gana da masu riƙe da madafun iko na ƙasar da suka je baƙunta.

Tinubu, Erdogan da wakilan gwamnatocin Najeriya da Turkiyya ana tattaunawa

Wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta, ya nuna lokacin da Tinubu ya yi tuntuɓe ya yi ƙasa sannan aka yi gaggawar kai masa ɗauki.

Tinubu ya kife a ƙasa ne yayin da suka jero suna tafe tare da takwaransa na Turkiyya, Recep Erdogan.

Hotunan bidiyo sun naɗo faruwar lamarin bayan kammala faretin tarba ta ban girma da aka yi wa shugaban na Najeriyar mai shekara 73, ya samu gagarumar tarba daga takwaransa na Turkiyya a wani biki da ya halarta a Ankara, babban birnin ƙasar.

Kazalika, a wani saƙo da Fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa, ta ce wani ƙarfe ne ya haddasa tuntuɓen shugaban ƙasar da bai ankara da shi a kan hanyar da yake wucewa ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, a jiya Litinin ce Shugaba Tinubu ya kama hanyar zuwa Turkiyya a yunƙuri na ƙarfafa dangartaka tsakanin ƙasashen biyu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce ziyarar za ta mayar da hankali wajen haɗin gwiwa a fannin tsaro, ilimi, zamantakewa, ƙirƙire da kuma harkokin jiragen sama.

Ana sa ran ƙasashen biyu za su gabatar da shawarwari kan harkokin siyasa, diflomasiyya, sadarwar, cinikayya da zuba hannu jari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *