Yadda Ake Zama Da Uwar Miji
Uwar mijinki tana da mutukar mutunci da daraja, domin mijin da kike takama da shi danta ne, ita ta dauki cikinsa wata tara, ta haife shi, ta raine shi, ta yi wahala da shi, har ya girma kika gan shi kika aure shi da hakoransa cif a baki, kafin ya aure ki babarsa ya sani da ‘yan’uwansa, yanzu kuma ga ki kin shigo cikin danginsu, sai ki ce uwarsa ita ce abokiyar gabarki? Wannan babban kuskure ne.
Yanzu ‘yan mata har sunaye suke sanya wa iyayen mazajensu, wai uwar miji musifa ce, uwar miji bala’i ce, uwar miji hawan jini ce, wa’iyazu Billah, wacce ta haifi uban ‘ya’yanki ita ce musifa, lallai kuwa kin dauko hanyar rusa auren ki. Dole ne ki mutunta ta, dole ne ki so ta, kuma ko kin ki, ko kin so matsayin uwa take a wurinki.
Ya ke ‘yar’uwata mai shirin shiga dakin mijinta ki sani, uwar miji mutumiyar kirki ce, uwar miji masoyiyar ki ce, uwar miji tana da mutunci a idonki, idan kin dauke ta a haka to ga wasu dabaru nan da za ki yi amfani da su wurin malllakar uwar mijinki ba boka ba malam.
Dabarun su ne:
1)- Ki mutunta ta, idan za ki gaishe ta ki gaishe ta da mutuntawa, idan za ki yi mata magana ki yi mata magana da mutuntawa. Wannan shi zai saka mata soyayyanki a cikin zuciyarta.
2)- Kyautata mata: Ki yi kokari wurin kyautata mata, kyauta wajen yin mata dinki idan kina da hali, yi mata girki, idan tana bukatar wani abu ki saya ki bata, idan abinci ne abin da ta fi sonsa za ki rika bata, idan ma ba unguwarku daya ba, sai ki rika yi ana aika mata da shi lokaci zuwa lokaci.
3)- Idan kina son ki sami karbuwa to fa ki kula da irin maganganun da za ki rika furtawa a gabanta, kada ki sake ki yi maganar da ba za ta so ba, idan ma kin yi ne kika ga ba ta so ba to sai ki nemi afuwarta.
4)- Ki rika ambata mata abin da danta ya ke yi na alkairi, misali idan yana tallafa wa wata makaranta, ko taimaka wa wasu gajiyayyu, kada ki rika ambata mata yana saya miki kaza da kaza domin wata uwar mijin sai ta fara hassada da tada hankalinta, ta ce kin mallake shi, ai sai abin da kika ce ya ke yi, shikenan sai ta tsane ki.
ZA MU CI GABA MAKO MAI ZUWA IDAN ALLAH YA KAI MU