Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje: Japan Ba Ta Da Ikon Yin Tsokaci Kan Batun Yankin Taiwan Na Kasar Sin

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Talata cewa, Japan ba ta da ikon yin tsokaci kan yankin Taiwan na kasar Sin, walau daga bangaren tarihi ko kuma abin da shari’a ta halasta, kana ya yi kira ga Japan da ta daina tayar da fitina kan batun yankin Taiwan.

Guo Jiakun ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na yau da kullum domin mayar da martani ga kalaman da firaministar kasar Japan Sanae Takaichi ta yi kwanan nan game da Taiwan.

A jiya Litinin, Takaichi ta ce idan wani lamari ya faru a mashigin tekun Taiwan, Amurka da Japan za su iya daukar mataki na hadaka don kwashe ’yan kasarsu, tana mai karawa da cewa Japan ba za ta yi biris da kawayenta a irin wannan yanayi ba.

A cewar Guo, kalaman da suka fito daga bangaren Japan kwanan nan sun sake fallasa manufar masu tsattsauran ra’ayi na kasar wajen tayar da rikici, da haifar da abubuwa masu cin tuwo a kwarya, don amfani da hujjar hakan wajen kara shan damarar amfani da karfin soji, da kuma kalubalantar tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu, inda ya kara da cewa irin wadannan take-taken sun yi matukar kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da kuma ginshikin siyasa na dangantakar Sin da Japan.

Kazalika, duk dai a taron manema labarun, a martanin da ya mayar ga tambayar da manema labarai suka yi cewa gwamnatin kasar Cuba ta yi Allah wadai da Amurka wadda aka ruwaito cewa tana tunanin kara tsaurara shamakance kasar Cuba ba bisa ka’ida ba, Guo Jiakun ya ce ya kamata Amurka ta dakatar da hana al’ummar Cuba ’yancinsu na rayuwa da samun ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *