Sojoji sun kashe ɗan bindiga a Kaduna

[ad_1]



Rundunar tsaron haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace (JTF OPEP) ta kashe wani ɗan fashi mai satar mutane a Ƙaramar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, bayan da sojojin suka gano mafakar ’yan ta’addan a garin Jagindi/Kogum da ke Kudancin Kaduna.

Sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Joshua Atu John, ta ce sojojin sun kai samamen ne bisa bayanan sirri da suka samu.

Sanarwar ta ce yayin musayar wuta da ’yan bindigar, sojojin sun kashe ɗaya daga cikin su mai suna Ɗahiru Adamu Barka, yayin da sauran suka tsere.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bin sawun waɗanda suka gudu domin tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar EF Oyinlola, ya yaba wa dakarun bisa nasarar da suka samu.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin tallafa wa ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *