AFCON 2026: Algeria Ta Lallasa Sudan Da Ci 3 Da Nema
[ad_1]
A wasa na biyu da aka buga a rukunin E na gasar ƙasashen nahiyar Afirika da ake ci gaba da bugawa a ƙasar Morocco, ƙasar Alkjeriya ta lallasa Sudan da ci 3-0 a filin wasa na Moulay Abdellah da ke birnin Rabat.
An gudanar da wasan a tsanake da nuna ƙwazo tsakanin ƙasashen biyu yayin da manyan tsoffin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa ciki har da Zinedine Zidane suka kalli wasan.
- Yadda Ake Inganta Tsarin Harkokin Kudi Na Dattawa A Kasar Sin
- INEC Ta Yi Watsi Da Shugabancin PDP Da Turaki Ke Jagoranta
Zinedine Zidane ya halarci wasan da yau da aka buga a Rabat domin ƙara ƙarfafa gwuiwar ɗansa, Luca Zidane wanda ke takawa ƙasar Algeria leda a matsayin mai tsaron raga.
Luca ta wakilci ƙasar Faransa a wasannin ƙasashe a matakin matasa ‘yan ƙasa da shekaru 23, 19 da 18 a shekarun baya.
Riyad Mahrez ne, ya zura wa Sudan ƙwallo a minti na biyu da fara wasa, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci tsohon ɗan wasan na Leicester da Manchester City ya zura ƙwallonsa ta biyu kafin Islam Maza ya zura wa Algeria ƙwallo ta uku.
Aljeriya ta ɗare saman teburin rukunin E tare da ƙwallaye uku da maki uku.
[ad_2]
Source link