BUK ta kori ɗalibai 171 kan amfani da takardun bogi
[ad_1]
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta kori ɗalibai 171 bisa bisa samunsu da laifin gabatar da takardun bogi wajen neman cancantar samun gurbin karatu a jami’ar.
Majalisar Gudanarwar jami’ar ce ta ɗauki matakin bayan zamanta karo na 433 da aka gudanar a ranar 4 ga Maris, 2026, bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin bincike kan batutuwan da suka shafi sahihanci da cancantar shiga jami’ar.
Rahoton ya gano cewa ɗaliban sun yi amfani da takardun bogi domin samun gurbin karatu, abin da ya saɓa wa sashe na 20.7 na dokokin jarrabawa da harkokin ilimi na jami’ar (GEAR), wanda ya tanadi hukuncin kora ga duk wanda aka samu da irin wannan laifi.
Haka kuma, majalisar ta amince da korar wani ɗalibi daga sashen injiniyan gine-gine, bayan an same shi da laifin kai hari ga masu lura da ɗalibai a lokacin jarabawa.
Jami’ar ta jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya da ɗa’a a harkokin ilimi, tana mai gargadin cewa duk wani saba doka zai fuskanci hukunci mai tsauri bisa ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link