Jam’iyyun adawa sun yi watsi da shirin ƙara wa ’yan siyasa albashi
[ad_1]
Manyan jam’iyyun adawa; PDP, NNPP da kuma ADC, sun yi Allah-wadai da shirin ƙara wa manyan ’yan siyasa albashi.
Hukumar Nazarin Ƙarin Albashi (RMAFC), ta sanar da shirin duba albashin Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, ministoci, gwamnoni da sauransu.
Hukumar ta ce ba a duba albashin ba tun 2008, don haka lokaci ya yi da za a gyara.
Sai dai jam’iyyun adawa sun ce wannan shiri ya nuna son zuciya, musamman a wannan lokaci da ’yan Najeriya ke fama da yunwa, tsadar rayuwa, da ƙarancin albashin Naira 70,000 wanda ba ya isar ma’aikata.
Mai magana da yawun ADC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya ce wannan shiri ya nuna rashin sanin halin da al’umma ke ciki.
“Ta yaya ’yan siyasa ke ke yin rayuwa ta alfarma idan har wannan albashin ba shi da wani tasiri a gare su?” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “Shirin ƙara musu albashi a lokacin da mutane ke fama da tsadar abinci, mai da ƙaracin albashi yana nuna raini ga talakawa. Wannan ba shugabanci ba ne; son kai ne kawai.”
Shugaban NNPP na Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya yi tir da wannan shiri.
“Rashin tausayi ne a ƙara wa ’yan siyasa albashi a lokacin da ma’aikata ke neman albashin da zai ishe su. Shugabanni na gaskiya su kan yi haƙuri wajen sadaukarwarsu ga jama’a ,” in ji shi.
Ya kuma kawo misalan wasu ƙasashe: “A wasu ƙasashe da ke fama da rikici, shugabanni su kan rage nasu albashin domin nuna goyon baya ga jama’a.
“Shugabannin Najeriya ma su yi haka, ba wai su ƙara wa kansu ba yayin da jama’a ke fama da wahalhalu,” in ji Ajadi.
Mataimakin Jagoran Matasa na PDP, Timothy Osadolor, ya kira yunƙurin da “rashin tausayi” da kuma cin amanar jama’a.
“Babban rashin tausayi ne a kawo wannan magana a lokacin da yunwa, hauhawar farashi da faɗuwar darajar Naira ya dabaibaye ƙasa.
“A irin wannan lokaci, abin da ya kamata shugabanni su tattauna shi ne yadda za a rage kashe kuɗaɗen gwamnati, ba wai ƙara kansu albashi ba,” in ji shi.
Ya kuma yi gargaɗin cewa wannan abu na iya tayar da hankulan jama’a.
“Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen rage wahalar da talakawa ke ciki. Duk wani yunƙuri na ƙara wa ’yan siyasa dukiya a irin wannan lokaci ba zai haifar da ɗa mai ido ba,” in ji shi.
Jam’iyyun ukun sun roƙi Gwamnatin Tarayya kan shirin ƙarin albashin, inda suka buƙaci ta mayar da hankali wajen ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata, rage kashe kuɗin gwamnati, da sauƙaƙa wa talakawa wahalhalun da suke fuskanta.
Ajadi na NNPP ya ce: “Abin da ƙasa ke buƙata yanzu shi ne yin taka-tsantsan a kan kuɗi, ba wai ’yan siyasa su ƙara cin moriya yayin da talakawa ke cikin wahala ba.”
Abdullahi na ADC ya ƙara da cewa: “Maimakon a ƙara wa manyan ‘yan siyasa dukiya, kamata ya yi duk wani shirin gwamnati ya mayar da hankali kan taimakon talakawa masu rauni.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link