Jam’iyyar NNPP ta naɗa Shugaban Riƙo a Kano

[ad_1]



Jam’iyyar NNPP ta naɗa Honorabul Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin sabon shugabanta na riƙo a Jihar Kano.

Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar ne ya sanar da naɗin Abiya a wani taron gaggawa a ranar Talata.

Wannnan naɗi ta zo ne a yayin da jam’iyyar ke cikin dabaibayi da rabuwar kai, game da shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, ko da magudun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bai so ba.

Kwamitin ya naɗa Abiya ne bayan karɓar rahoton korar tsohon Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa, daga shugabannin mazaɓarsa.

Aminiya ta ruwaito cewa ranar Litinin da dare shugabannin NNPP na mazaɓar wato Gargari da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, sun sanar da korar Hashimu Dungurawa kan zargin haddasa rikici a jam’iyyar da kuma yi mata zagon ƙasa.

Bayan karɓar rahoton daga Shugaban Jam’iyyar na ƙaramar hukumar, majalisar amince da shi.

Uban Iya bayyana cewa an ɗauki matsayar ne tun mako biyu bayan babban zaɓen da ya gabata.

Kwamitin zartaswar ya karbi rahoton tare da amince s’da shawarwarin da ke ciki, gami da tabbatar da naɗin Abiya a matsayin shugaban riƙo, domin tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.

A jawabinsa, Honorabul Abdullahi Zubairu Abiya ya bayar da tabbacin yin adalci ko kowane ɗan jam’iyyar NNPP da kuma cikakken biyayya ga jagoran Jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *