Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
[ad_1]
Gwamna Peter Mba na Jihar Enugu da kwamishinoninsa da sauran mukarrabansa sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
Da yake sanar da hakan a ranar Talata a garin Enugu, Gwamna Mbah ya jaddada aniyarsa ta kare muradun jihar, tare da bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta ba wa jihar karin damar hadin gwiwa domin samun ci-gaba.
Mbah, wanda ya samu rakiyar magabacinsa, tsohon Gwamna Ifeanyi Ugwanyi, da ’yan majalisar dokokin jihar da takwarorinsu na Majalisar Dokoki ta Kasa ya ce sun yi ittifafkin komawa APC ne domin kara hidimta wa al’ummar jihar da kuma kare manufofinta na ci gaba.
“Bayan tsawon lokaci ana ta nazari, a yau dai, mun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC. Wajibi ne mu ci gaba a kan muradunmu na ci gaba.
“Na fahimci cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, abonkin tafiya ne ta fuskar manufa, kuma jajirtaccen mutun ne mai hangen nesa da ke daukar matakan da za su amfane mu a na gaba,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Wannan shawara ce a muka dauka a dunkule — ’yan majalisar dokokin jiha da majalisar dokoki ta kasa da Majsaliar Zartaswa ta jiha daukacin shugabannin kananan hukumomi da masu rike da mukaman siyasa da kimanin kashi 80 na shugabannin jam’iyya.”
Duk da cewa ya bayyana godiya ga PDP da gudummawarta a lokacin zabensa, amma ya koka da cewa “yawanci ba a sauraron muryarmu” idan wani sha’ani ya taso da ya shafi yankin Kudu maso Gabas.
Ya bayyan kwarin gwiwa cewa hadewarsa da APC zai taimaki ci-gaban Jihar Enugu da ma Najeriya baki daya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link