Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Koma APC
[ad_1]
Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya bayyana aniyarsa ta yin aiki domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
Ɗan Atikun, Wanda aka fi sani da “Abba”, an tarɓe shi a ranar Alhamis a Majalisar Tarayya da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da manyan shugabannin APC daga shiyyar Arewa maso Gabas.
- Atiku Ya Fara Neman Mulki Tun Ina NYSC – Datti Baba-Ahmed
- Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano
Da yake sanar da sauya sheƙarsa, Abba ya ce ya yi murabus daga jam’iyyar PDP, ya kuma yanke shawarar shiga APC bisa abin da ya kira kyakkyawan jagoranci da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Tinubu. Ya ce zai yi aiki tare da Sanata Barau domin tabbatar da wa’adin mulki na biyu ga Tinubu a 2027, tare da umartar dukkan mambobin ƙungiyarsa su shiga APC su goyi bayan Ajandar “Sabunta Fata“.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyarsa ta siyasa da ya kafa a 2022, wato Haske Atiku Organisation, za ta sauya suna nan take zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken daidaituwar manufofin APC gabanin zaɓen 2027. Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Comrade Mustapha Salihu, ya bayyana wannan sauyin sheƙa a matsayin alama mai nuni da tabbatar ƙasa kyawawan manufofin APC.
A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya taya Abba murna bisa matakin da ya kira jarumta da hikima, yana mai cewa ya yanke wannan shawara ne bisa aƙida da imani da manufofin Shugaba Tinubu. Ya ƙara da cewa Abba, wanda ya kasance yana bibiyar siyasar Nijeriya daga Amurka, ya dawo ne domin ba da gudummawa wajen gina makomar ƙasa.
A ƙarshe, wakilan ƙungiyarsa daga Kano sun tabbatar da cewa za su ƙara zage damtse wajen tallata APC da tabbatar da nasararta a zaɓen 2027.
[ad_2]
Source link