Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni

[ad_1]



Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya shawarci matasa da ‘yan siyasa masu tasowa da su fahimci cewa siyasa ba ta tafiya da rowa, illa da juriya, sadaukarwa da biyayya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin rantsar da sabon Alƙalin Alƙalai na jihar (Grand Khadi), tare da wasu mashawartarsa na musamman, mamba na dindindin a hukumar SUBEB da kuma sabbin sakatarorin dindindin guda 13, a wani taro da aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu.

A jawabinsa, Buni ya ce matasa da ‘yan siyasa masu neman makoma a fagen shugabanci dole ne su kasance masu haƙuri, biyayya da ƙwarewa tare da ɗa’a, domin samun ci gaba.

“Siyasa aiki ne na haƙuri, biyayya da sadaukarwa. Ba za a cimma nasara da rowa ko gaggawa ba. Idan matasa suka rungumi juriya, gobe su ma za su zama shugabanni a matakai daban-daban,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa siyasa tana buƙatar haɗin kai, fahimta da tsayin daka wajen bauta wa al’umma, ba don amfanin kai kaɗai ba, lamarin da ya ce shi ne ginshiƙin da ya kamata kowane ɗan siyasa ya ɗora kansa a kai.

Gwamnan ya kuma ja hankalin sabbin jami’an da aka rantsar da su kasance masu gaskiya, nagarta da aiki tuƙuru wajen tabbatar da nagartaccen tsarin mulki a Jihar Yobe.

“Aikin da aka ba ku nauyi ne daga Allah da kuma al’umma. Ku tabbatar da gaskiya, aminci da sadaukarwa, domin idan kuka yi haka, za ku bar tarihi mai kyau a Jihar Yobe,” in ji shi.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai da dimbin jama’a daga sassa daban-daban na jihar, inda aka yaba wa Gwamna Buni bisa namijin ƙoƙarinsa na gina al’umma mai dogaro da kai da kuma inganta shugabanci nagari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *