Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang
[ad_1]
Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.
Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
A jiya Asabar ce jam’iyyar ta kori ministan, wanda ya daɗe yana rigima da shugabancin jam’iyyar, da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayin babban taronta na ƙasa tana mai zargin su da yi mata zagon ƙasa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Muftwang ya ce majalisar gwamnonin PDP da kwamatin zartarwa ba su tattauna batun ba kafin a bijiro da shi yayin taron.
Ya ƙara da cewa “korar jiga-jigan jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci ba shawara ce mai kyau ba wajen shawo kan rikicin da ya dabaibaye PDP.”
Kalaman Muftwang na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri shi ma ya ce bai goyi bayan korar Ministan Abujan da abokan siyasarsa ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link