Rikicin Masarauta Ya Kusa Zuwa Ƙarshe — Gwamnatin Kano

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa rikicin masarautar jihar da ya shafe shekaru ana yinsa, ya kusa zuwa ƙarshe.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ne, ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a jihar.

  • Kotu Ta Ware Kwanaki 10 Don Kammala Shari’ar EFCC Da Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele
  • CAF Ta Ci Tarar Senegal Da Morocco Kan Haddasa Rikici A Wasan Ƙarshe Na Gasar AFCON

Waiya, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace domin kawo ƙarshen rikicin tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shirya tuntuɓar masu ruwa da tsaki da duk waɗanda ya kamata a nema domin tattaunawa tare da nemo mafita nan gaba kaɗan.

Ya ce za su ɗauki matakin da ya dace ta hanyar bin dokokin da suka kamata musamman waɗanda suka yi magana a kan masarautu da kuma abin da al’ummar jihar suka fi so.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *