2027: Gwamnan Bauchi Na Shirin Komawa ADC, Bayan Kasa Shawo Kan Rikicin PDP


Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, na duba yiwuwar komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Gwamnan ya nuna haka ne a ranar Talata lokacin da gwamnan ya karɓi bakwancin tawagar ADC ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, a Ramat House da ke Bauchi.

  • Kotu Ta Ɗage Sauraron Neman Beli Na El-Rufai Zuwa Gobe Laraba
  • Jakadan Sin a Najeriya Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Aikin Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Najeriya

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da rikici cikin gida suka mamaye jam’iyyar PDP lamarin da ya har ya sanya a kwanakin baya aka yi ta yada cewa gwamnan zan koma APC, lamarin bai yiyu ba inda yanzu kuma alƙiblar ta koma kan ADC. Hakan dai bai rasa nasaba da rikicin tsakanin ɓangaren Nyesom Wike da su ta Bala Muhammad.

Da ya ke magana a yayin taron, Gwamna Muhammad ya ce tawagarsu ta yi zurfin tunani da tuntubar bangarori daban ciki har da APC, amma sun fahimci cewa ba za su iya ci gaba da zama a inda ba a maraba da su ba. Don haka ne suka maida hankali wajen duba yiyuwar komawa cikin jam’iyyar ADC domin ci gaba da gudanar da harkokin siyasarsu a ciki.

Gwamnan ya bayyana ADC a matsayin jam’iyya mai inganci kuma mai jan hankali, yana mai cewa tana ƙara samun karɓuwa daga masu ruwa da tsaki da suke tattaunawa da ita, tare da al’ummar ƙasa.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu tattaunawa na ci gaba kuma ba a kai ga cimma matsaya ta ƙarshe ba.

“Ya zuwa yanzu, ADC ita ce zaɓinmu na farko, amma ba mu kammala tattaunawa ta yadda za ta tabbatar da cikakken haɗin kai da masu ruwa da tsaki ba. Muna son kauce wa yin kuskure,” don haka ya nuna cewa dole su ƙara zurfafa tuntuɓa a tsakanin sauran masu ruwa da tsaki da ‘yan tawagarsu domin tafiya tare.

Gwamna Muhammad ya bayyana cewa a matsayinsa na jagora a jihar Bauchi da ma ƙasa dole ne ya nemi jin sauran bangarori domin tafiya tare don neman wa jama’a mafita.

“Dole ne mu yi komai a hankali. Muna buƙatar daidaita muradun masu ruwa da tsaki a matakan ƙasa da jiha, shi ya sa tattaunawa ta ɗauki lokaci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tawagarsa a shirye take ta yi haɗaka da ADC, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tare da wasu jam’iyyun siyasa, domin duba wacce ta fi dacewa da tawagar tasu.

“Mun nuna shirye-shiryenmu na shiga tare da su bisa yarjejeniya. Ko da yake ba a kammala tattaunawa gaba ɗaya ba, ADC ce har yanzu zaɓinmu a halin yanzu” ya bayyana.

Gwamnan ya gode wa shugabannin ADC bisa gayyatar da suka miƙa masa, yana mai cewa hakan ya zo a kan lokaci duba da ƙalubalen siyasa da ake fuskanta.

“Idan kana fuskantar ƙalubalen siyasa masu tsanani kuma wani ya miƙa maka hannu na haɗin gwiwa, ya dace ka nuna godiya. Amma har yanzu muna mai da hankali ne kan lashe zaɓe, wanda a ƙarshe ke faruwa a rumfunan zaɓe,” in ji shi.

Ya kuma jaddada buƙatar dabarun neman mafita a siyasa da haɗin kai, yana mai cewa halin da ake ciki a jam’iyyar PDP a halin yanzu ba yanayi ne da zai haifar da sakamakon mai kyau ba.

“Don haka dole ne mu fuskanci gaskiyar halin da ake ciki mu kuma duba wannan damar da ADC ta bayar. Ba za mu yi wasa da wannan damar ba,” ya ƙara da cewa.

Gwamna Mohammed ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitoci biyu, ɗaya a matakin ƙasa a Abuja, ɗaya kuma a Bauchi domin nazarin alkiblar siyasarsu da kuma tunƙarar yadda za a yi zaɓukan da suke tafe a cikin jam’iyyu daban-daban.

“Za ku ji cikakken matsayarmu a ranar Alhamis bayan taronmu a Abuja,” in ji shi.

Tun da farko, jagoran tawagar ADC, Babachir David Lawal, ya ce ziyarar tasu ta zo ne bisa umarnin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, David Mark, domin gayyatar Gwamna Bala Mohammed ya shiga ADC gabanin zaɓen 2027.

Ya bayyana gwamnan a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa mai tasiri, yana mai cewa shigarsa jam’iyyar zai ƙara ƙarfinta da damar lashe zaɓe.

Lawal ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun adawa, yana mai gargadin cewa rashin haɗin kan domin tunƙarar kalubalen da suke jibge iya haifar da barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Taron na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Gwamna Bala Mohammed ya kira taron masu ruwa da tsaki na PDP a Bauchi, domin magance saɓanin cikin gida da ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *