An gurfanar da mutum 4 a kotu kan zargin sace matar aure a Kano
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta umarci a ci gaba da tsare wasu mutum huɗu da ake zargi da sace matar aure a unguwar Sauna da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar.
An gurfanar da waɗanda ake zargin; Usman Kafada Kwata, Shafiu Adamu, Jamilu Akilu, da Muhyedeen Warawa, kan laifukan da suka shafi haɗin gwiwa, fashi da makami, da sace mutum.
Masu gabatar da ƙara sun ce waɗanda ake zargin sun kai hari tare da sace Aisha Usaini a gidanta ta hanyar amfani da makamai.
Sun tsare ta na tsawon kwanaki tara kafin su sake ta, biyo bayan biya kuɗin fansa Naira miliyan biyar da iyalinta suka yi.
Alƙalin kotun, Justice Maryam Sabo, ta umarci lauyan jihar, Barista Lamido Abba Sorondinki, ya gabatar da shaidu a zaman kotu na gaba.
Kotun ta ce a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin har zuwa lokacin sauraron shari’ar a ranar 19 ga watan Fabrairu.