Kotu Ta Ware Kwanaki 10 Don Kammala Shari’ar EFCC Da Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

[ad_1]

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da ƙarin kwanaki 10 domin kammala shari’ar cin hanci da rashawa da Hukumar EFCC ke yi wa tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan batun sauya fasalin Naira.

Mai shari’a Maryann Anenih ta ware ranakun ne bayan lauyoyin EFCC da na Emefiele sun amince da jadawalin sauraron shari’ar.

  • Yajin Aiki: Duk Wanda Ya Ƙi Komawa Aiki Bayan Umarnin Kotu Zai Fuskanci Hukunci – Wike
  • Yadda Shugaba Tinubu Ya Yi Tuntuɓe Ya Faɗi A Turkey

An fara shari’ar tun a shekarar 2024, kuma ana sa ran za a kammala ta tsakanin Fabrairu da Yunin 2026.

A zaman kotun, wani shaidan EFCC ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sauya fasalin Naira.

Amma ya bayar da umarni cewa a riƙa buga sabbin takardun kuɗin a cikin Nijeriya, ba a ƙasashen waje ba.

Emefiele ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa, kuma kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari’ar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *