An yi wa yarinya ’yar shekara 15 kisan gilla a Gombe
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta tabbatar da rasuwar wata yarinya mai suna Aisha mai shekaru 15 a garin Kwami, bayan ɓacewarta kwanaki kaɗan.
An gano gawarta a cikin wani rami kusa da ƙauyukan Wakili da Tuguji.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Aisha ta tafi sayen wake da yammacin ranar Litinin, daga nan ta ɓace ba ta dawo gida ba.
“Babanta, Malam Abubakar, ya kai rahoton ɓacewarta a ranar Talata da misalin ƙarfe 12 na rana. Ya ce ta tafi sayen wake da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin ranar Litinin amma bata dawo ba.
“Abin takaici, an tsinci gawarta a cikin daji a kusa da ƙauyen,” in ji Abdullahi.
’Yan sanda sun ziyarci wajen da aka samu gawar kuma sun lura da akwai alamun an gana maga azaba.
An ɗauke gawarta zuwa asibiti domin gudanar da binciken likitoci.
’Yan sandan suna gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da kama su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link