Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna

[ad_1]



Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa, reshen Giwa.

Rahoto ya bayyana cewa Malam Kabiru ya rasu ne yayin aikin ceto wasu mutane da ’yan fashi suka sace daga yankin Danja na Jihar Katsina.

Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa, Kwamanda Usman Taju, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, jim kaɗan bayan jana’izar marigayin.

Ya ce: “Da safiyar Asabar muka samu labarin cewa ’yan fashi sun yi garkuwa da wasu maza da mata daga Danja, suka shigo da su Giwa. Nan take muka haɗu domin ceto su.

“Mun samu nasarar ceto mata uku daga hannun ’yan fashin, amma abin baƙin ciki, ɗaya daga cikinmu, Malam Kabiru Gangara, ya rasa ransa yayin aikin.”

Usman Taju, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a kan aikin kare rayuka da dukiyar jama’a, inda ya ce hakan babban abin alfahari ne.

Ya roƙi gwamnatin Jihar Kaduna da ta taimaka musu da kayan aiki da horo, domin ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

“Haƙiƙa muna fama da ƙalubale da dama, amma hakan ba zai hana mu ci gaba da kare jama’a ba,” in ji shi.

Kwamandan ya nemi gwamnati ta riƙa kula da iyalan jami’an da suka rasu a bakin aiki, domin hakan zai bai wa sauran maharba ƙwarin guiwa.

Marigayin ya rasu ya bar mata uku da yara shida, kuma an binne shi a ƙauyensu na Gangara, a Jihar Kaduna.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *