Sin Na Matukar Goyon Bayan Tsarin Gudanar Da Duniya Na Yanzu
[ad_1]
Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa wadanda suke birnin Vienna na Austria, Li Song ya ce, Sin a shirye take ta karfafa tattaunawa, da hadin gwiwa da hukumomin kasa da kasa da kasashe membobinsu, tana kuma matukar goyon bayan tsarin gudanar da duniya na yanzu, da burin kyautata iko da matsayin MDD.
Li ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da yake tsokaci gaban mahalarta liyafar murnar zuwan ranar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa, da aka gudanar a helkwatar MDD dake birnin na Vienna.
Jami’in ya kara da cewa, shawarar inganta jagorancin duniya da kasar Sin ta gabatar, na kunshe da dabarun kasar na gina tsarin gudanarwa na duniya mai tattare da karin adalci da hangen nesa, wanda zai taimaka wajen farfado da muhimmin matsayin MDD, da rawar da take takawa ta jagoranci.
Ya ce Sin za ta himmatu wajen ingiza dawo da batutuwan samar da ci gaban tsakiyar ajandar jagorancin duniya, da kyautata wakilci, da daga muryoyin kasashe masu tasowa, da bayar da gagarumar gudunmawa ga burikan MDD na wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba.
A nasa tsokaci kuwa, babban daraktan hukumar bunkasa masana’antu ta MDD Gerd Mueller, cewa ya yi tsarin jagorancin duniya na yanzu da MDD ke goyon baya na fuskantar matsin lamba, kuma rawar da Sin ke takawa na da matukar muhimmanci, a matsayinta na daidaitacciyar abokiyar hulda ga tsarin aiwatar da manufofin MDD a duniya, da ayyukan samar da daidaito da zaman lafiya da ’yanci. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link