Carlos Alcaraz ya kai wasan kusa da na ƙarshe a Australian Open
[ad_1]
A karon farko a tarihinsa na wasan tennis, Carlos Alcaraz ya kai wasan daf da na ƙarshe a gasar Australian Open da ake fafatawa a birnin Melbourne na ƙasar Australia.
Alcaraz, wanda ke matsayi na ɗaya a duniya, ya samu nasarar ne bayan ya doke Alex de Minaur da ci 7-5, 6-2, 6-1 a wasan kwata fainal.
Hakan dai na nufin ɗan wasan na ƙasar Sifaniya zai fafata a wasan daf da ƙarshe da Alexander Zverev, wanda shi ma ya samu gurbin ne bayan ya fitar da Learner Tien a daren jiya Talata.
A yau Laraba kuma, aka ci gaba da wasannin zagayen kwata fainal, inda Novak Djokovic, wanda ya lashe kofin gasar sau 10, zai kara da Lorenzo Musetti.
A ɓangaren mata kuwa, Elina Svitolina ta kai matakin daf da na ƙarshe bayan ta doke Coco Gauff da ci 6-1, 6-3 cikin mintuna 59.
Wannan ne karo na farko da Svitolina ta kai wasan daf da ƙarshe a gasar Australian Open, kuma za ta kara ne da Aryna Sabalenka, wadda ta doke Iva Jovic da ci 6-3, 6-0.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link