An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan a Akwa Ibom

[ad_1]



An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan.

Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar Naira 500,000, waɗanda suka samu Azurfa Naira 250,000, yayin da waɗanda suka lashe Tagulla suka tashi da Naira 150,000.

A jawabinsa na rufe gasar da aka gudanar a filin wasa na Uyo, babban birnin jihar, Gwamna Eno ya bayyana cewa dukkan ’yan wasan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 31 na jihar.

Baya ga kyautar da ’yan wasa suka samu, gwamnan ya bai wa kowace ƙaramar hukuma da ta halarci gasar Naira miliyan 15.

Haka kuma, waɗanda suka yi wa sauran zarra sun samu Naira miliyan 10, yayin da sauran ƙananan hukumomin kuma kowacce ta samu Naira miliyan 5 a matsayin tallafi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *