Real Madrid ta koma saman teburin La Liga
[ad_1]
Real Madrid ta koma saman teburin gasar La Liga bayan da ta doke Villarreal da ci 2-0 a wasan da aka buga ranar Asabar.
Kylian Mbappe ne ya ci ƙwallaye biyu a wasan da Villarreal ta karɓi baƙunci, inda hakan ya kai adadin ƙwallayensa a La Liga zuwa 21 a kakar bana, yayin da jimillar ƙwallayensa a dukkan gasa ta kai 34.
Mbappe ya fara jefa ƙwallon farko ne mintuna kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kafin daga bisani ya ƙara ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida ana daf da tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon, Real Madrid ta bai wa abokiyar hamayyarta Barcelona tazarar maki biyu, wadda za ta karɓi bakuncin Real Oviedo ranar Lahadi.
Wannan shi ne karo na uku a jere da Real Madrid ke samun nasara a dukkan gasa, lamarin da ke nuna farfaɗowar ƙungiyar ƙarƙashin sabon koci, Alvaro Arbeloa, wanda ya karɓi ragamar jagoranci bayan maye gurbin Xabi Alonso.
Galabar da aka yi kan Villarreal ta bar ƙungiyar a matsayi na huɗu, da tazarar maki 10 a bayan Real Madrid, duk da tana da kwantan wasa ɗaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link