Ministan sufuri ya yi murabus domin yin takarar gwamna
[ad_1]
Ministan Sufuri Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ya ajiye muƙaminsa domin takarar Gwamnan Jihar Gombe.
Da haka ya shiga jerin jami’an Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da suka ajiye mukamansu domin neman takara a zaben shekarar 2027.
Ya ajiye mukamin nasa ne sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da shugaban kasa ya ba wa jami’an gwamnatinsa da ke da muradin tsayawa takara su ajiye mukaminsu.
Sauran ministocin da suka ajiye mukamansu sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ahmed Tuggar, wanda ke neman fitowa takarar Gwamnan Jihar Bauchi da kuma Karamin Minista, Sununu da ke son fitowa takarar dan majalisar dokoki ta kasa a Jihar Kebbi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link