Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru a kotu a yau Alhamis.

Za a gurfanar da su ne a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Mutanen da za a gurfanar su ne Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da mataimakinsa Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Mahmud Al-Nigeri ko Mallam Mamuda.

Za su fuskanci tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci.

Tuhuma ta farko ta ce, mutanen sun taimaka wajen tsara da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru tsakanin 2013 zuwa 2015.

An haramta ayyukan Ansaru a Najeriya kuma tana da alaƙa da Al-Qaeda.

Abu Bara’a wanda yake ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Okene a Jihar Kogi ne, yayin da Mahmud Al-Nigeri ya fito daga Ƙaramar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.

An kama su ne yayin wani samame da hukumomin tsaro da na leƙen asiri suka gudanar tsakanin watan Mayu zuwa Yulin 2025.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne, ya bayyana kama su a ranar 16 ga watan Agusta, a Abuja.

Ana zargin Ansaru da kai hare-hare da sace mutane masu yawa a faɗin Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *