Sin Ta Ce Ikirarin Japan Cewa Matsayarta Kan Batun Taiwan Ba Ta Sauya Ba, Bai Wadatar Ba
[ad_1]
Kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, ikirarin Japan cewa matsayarta game da batun Taiwan ba ta sauya ba, bai wadatar ba, tana mai kira ga Japan din ta fayyace ko har yanzu tana rike da manufar Sin daya tilo, kuma ta gyara kalamai na kuskure da ta furta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau, lokacin da take martani ga wata sanarwar da gwamnatin Japan ta fitar. Sanarwar ta bayyana cewa kalaman firaminista Sanae Takaici na baya bayan nan, ba su sauya matsayar da Japan ta dade tana rike da ita ba.
A cewar Mao Ning, nanata cewa matsayar Japan ba ta sauya ba, bai magance ainihin batun ba. Ta ce abun da Sin da kasa da kasa suke son sani shi ne, wace matsaya ce Japan ke ikirarin tana rike da ita? Shin har yanzu Japan na amincewa da manufar kasar Sin daya tilo? Ya kamata Japan ta bayar da amsa daidai kuma bisa gaskiya, kuma ta yi cikakken bayani game da abun da take nufi da matsayarta bata sauya ba dangane da batun Taiwan.
Mao Ning ta bukaci Japan ta dauki matsayar kasar Sin da muhimmanci, ta kuma nazarta tare da gyara kuskurenta, ta janye kalamai na kuskure da ta yi, kana ta girmama alkawarin da ta yi wa Sin ta hanyar kwararan matakai. (FMM)
[ad_2]
Source link