Arewa Maso Gabashin Jigawa: Abokan Babandede Sun Dauki Harama

[ad_1]

Kungiyar abokan tsohon shugaban hukumar shige da fice ta kasa (NIS), CGI Babandede mai ritaya (FOMB) da ke yakin ganin ya zaman sanata a yankin arewa maso gabashin Jigawa sun dauki harama wajen ganin hakarsu ta cimma ruwa.

Kungiya ta kasance ta abokai da magoya baya da abokan aiki da kuma ma’aikatan da suka taba aiki karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar NIS), CGI Babandede mai ritaya, wanda shi ne shugaban hukumar na 16 wanda ya zamanatar da aiki hukumar a karkashin jagorancinsa.

  • 2027: Dole Dattawan Arewa Su Hada Kai Domin Samar Wa Yankin Mafita —Alhaji Babangida Aliyu
  • Ronaldo Ba Shi Da Ikon Yanke Hukunci A Gasar Saudi Pro League – Mahukunta

Me ya sa Muhammad Babandede yake da muhimmanci na musamman?

A tsakanin shekarun 2017 zuwa 2021, ya sauya tsarin aiki da gudanarwa na hukumar shige da fice ta Nijeriya ta hanyar fasahar zamani, har ta zama hukuma mai kima da ake misali da ita a duk fadin Afirka.

Nijeriya ta zama kasa ta farko a Afirka da ta kaddamar da amfani da ingantaccen tsarin yin fasfo na zamani, inda aka fara ba wa tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo (SAN), fasfo dinsu a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Wannan ya nuna kaddamar da ingantaccen fasfo nazamani shi ne irinsa na farko a Afirka a shekarar 2019.

Haka kuma, an samar da tsarin nan na e-bisa da biyan kudi ta intanet (online payment) don fasfo da sauran ayyukan da hukumar ke bayarwa ga jama’a a zamanance kuma a saukake.

An kuma gabatar da na’urar auto-gate a wasu manyan filayen jiragen sama na kasa da kasa, tare da tsarin sa ido da gudanarwa ta intanet kan shigowa da hana shigowa ga matafiya na kasashen waje gwargwadon hali.

Wannan ya taimaka wajen inganta matsayin tsaron shige da fice na Nijeriya a idon duniya, ta hanyar kama mutane da suka karya doka da hana tafiye-tafiye ba bisa ka’ida ba da hana shigowa kasar barkatai da kwace fasfo na manyan mutane masu matsayi a siyasa da iyalansu bisa ka’idojin hukumar da kuma yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da sauran hukumomin tsaro da ma’aikatun gwamnati ciki har da ONSA, NPF, EFCC, ICPC, DFIU, Sojoji, DSS, NIA, DIA da sauransu, domin kare muradun kasar nan.

An kuma gabatar da tsarin gudanar da kundaye ta lantarki a hukumance domin adanawa da karba da sarrafawa da amincewa da wasiku ta hanyar lantarki.

Wannan ya rage bata lokaci da karfin aiki, tare da kawar da jinkiri da bacewar wasu kundaye da aka adana su yayin da aka yi kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana da ingantaccen aiki.

Haka kuma ana samar da rahoton shekara-shekara tare da raba shi ga fadar shugaban kasa da sauran ma’aikartu da hukumomin gwamnati da rundunar sojoji da hukumomi da masu gudanarwa domin tantancewa da bitar ayyukan hukumar a kowacce shekara.

Baya ga wadannan kuma, ana fitar da mujallar hukumar mai taken “Gatekeepers” kowane wata, ana raba wa fadar shugaban kasa da ma’aikatun gwamnati da ofisoshin jakadanci da sojoji da hukumomi da masu samar da hidima da kuma jama’a, domin wayar da kai da bayar da bayanai kan ayyukan hukumar shige da fice ta Nijeriya.

Muhammad Babandede ya zamanantar da hukumar shige da fice ta karni na 21, tare da gina ginin fasaha irinsa na farko a hedikwatar hukumar da ke kan titin zuwa filin jirgin saman a kasa da kasa da ke Abuja.

Haka kuma, ya bar kwararrun jami’ai da ma’aikata masu kwazo da jajircewa da ke aiki da jami’an tsaron hadin gwiwa (JTF) da masu lura da kan iyakokin kasa da shingayen binciken ababen hawa da muhimman wuraren tsallaka iyaka.

Sannan kuma Muhammad Babandede ya kafa cibiyar kula da tsaro mai inganci a hedikwatar hukumar kula da shige da fice ta kasa domin sa ido kan ayyukan jami’ai da zirga-zirgar iyaka a kokarin amfani da sabbin fasahohi domin sintiri da kula da iyakokin Nijeriya.

Kamar yadda tsohon mai magana da yawun hukumar NIS kuma shugaban kafar sadarwa ta Hallbibe, James Sunday, FCAI, MNIIA ya rubuta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *