An rufe makarantu a Katsina da Taraba

[ad_1]



Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja.

Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro.

Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar.

Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari.

Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta.

Hakan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da sanarwar rufe dukkan makarantun gwamnatin, har sai abin da hali yayi.

Sanarwar da ta fito daga Hukumar Ilimin Firamare da Sakandaren jihar a ranar juma’a ta ce, ya ce makarantun za su kasance a rufe har sai an ga ci-gaban da aka samu na yanayin matsalar tsaron da ake fuskanta.

Gwamnatin tace tana nan tana bibiyar yadda sha’anin tsaron yake gudana kafin ɗaukar mataki na gaba.

Waɗannan matakai na zuwa ne bayan ’yan bindiga sun sace ɗalibai kimanin 340 a cikin mako guda a makarantun kwana a jihohin Kebbi da Neja.

A ranar Juma’a aka sace ɗalibai da malamai 315 a makarantar kwana ta St Mary da ke Jihar Neja, kwana huɗu bayan a ranar Litinin sun sace dalibai mata 26 suka kashe jami’an tsaro biyu a makarantar ’yan Mata ta Gwamanti GGCSS da ke yankin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu ta Jihar Kebbi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *