Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da  Biyan Biliyan 19 Don Ci Gaba da Aikin Titin Kano–Gwarzo–Dayi — Barau

[ad_1]

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 19 domin ci gaba da aikin titin Kano–Gwarzo–Dayi, wanda ya tsaya sama da shekaru uku.

Barau ya ce amincewar na daga cikin manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na farfaɗo da muhimman ayyukan more rayuwa. Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan ganawarsa da Mataimakin Manajan Darakta na kamfanin CGC Nigeria Limited, Lv Haiming, a Abuja, inda aka warware matsalolin da suka janyo tsaikon aikin.

  • Sanata Barau Ya Ziyarci Sansanonin Sojoji 4, Ya Buƙaci Murƙushe Ƴan Ta’adda
  • Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Ya ce an kammala dukkan shirye-shirye, an kuma bai wa kamfanin kwangilar Naira biliyan 19 domin komawa wurin aiki, yana mai cewa an riga an kammala shirye-shiryen dawo da ma’aikata filin gina titin.

Sanatan ya bayyana titin a matsayin muhimmiyar hanyar da ke haɗa al’ummomi a Jihar Kano da makwabtanta, yana mai cewa kammala aikin zai inganta zirga-zirga da kasuwanci, musamman safarar amfanin gona daga karkara zuwa kasuwanni.

A shekarar 2021 ne aka ƙaddamar da aikin gina titin mai tsawon kusan kilomita 100 a matsayin hanya mai layi biyu, kan kuɗi Naira biliyan 62.7, amma aikin ya tsaya tsawon lokaci. Al’ummomin yankin sun taɓa yin barazanar kai ƙara Majalisar Dokoki sakamakon tsaikon da aka samu wajen sakin kuɗaɗen kammala aikin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *