Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a hukumance.
Atiku wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar kujerar shugaban ƙasar Zaɓen 2023, ya karɓi katin ya yi rajistar zama tabbataccen ɗan jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.
Ya sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotuna riƙe da katin sabuwar jami’yyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam’iyyar a hukumance.
A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa Atikun ya bayyana ficewa daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
Tun a wancan lokacin dai Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam’iyyar ta PDP bisa la’akari da yadda ta sauka daga tubalinta na asali.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link