AFCON 2026: DR Congo To Yi Wa Senegal Fankale
[ad_1]
An buga kunnen doki a wasan mako na biyu da aka buga a rukunin D tsakanin ƙasashen Senegal da Dimokuraɗiyyar Congo a wasan kofin ƙasashen nahiyar Afirika da ake bugawa a ƙasar Morocco.
Duka ƙasashen biyu suna da maki huɗu yayin da suka buga wasanni biyu a gasar.
- Kanu, Salah, Drogba Da Manyan ‘Yan Wasan Da Ba Su Taba Lashe Kofin Afirka Ba
- Sayar Wa Yankin Taiwan Makamai Da Amurka Ta Yi: “Taimaka Masa” Ne Ko “Illata Shi”?
Senegal ta shiga wasan da ƙwarin gwiwa bayan ta yi nasara a kan Botswana da ci 3-0 a wasan farko, haka ita ma Dimokuraɗiyyar Congo wadda ta samu nasara da ci 1-0 a wasansu da Jamhuriyar Benin, inda ta jefa ƙwallo mai cike da ce-ce-ku-ce wadda ta haifar da muhawara tsakanin magoya baya da masu sharhi.
Dimokuraɗiyyar Congo ce ta fara zura ƙwallo a minti na 61 ta hannun Cedric Bakambu, amma Senegal ta mayar da martani minti 8 tsakani inda tauraron ɗan wasan gaban Senegal Sadio Mane ya farke kwallon a minti na 69.
Duka ƙasashen biyu za su jira har zuwa wasan ƙarshe domin sanin makomarsu a gasar.
Senegal za ta kece raini da Jamhuriyar Benin a wasanta na ƙarshe a rukunin, yayin da Dimokuraɗiyyar Congo ke fatan samun nasara a wasan da za ta buga da Botswana.
[ad_2]
Source link