Babu tattaunawa tsakanin Kwankwaso da APC —Kwankwasiyya

[ad_1]



Kungiyar Kwankwasiyya ta karyata rahotannin da ke cewa jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana tattaunawa da Jam’iyyar APC domin sauya sheka zuwa cikinta.

Kakakin kungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya fitar, ta bayyana cewa Kwankwaso bai taba shiga shiga tattaunawa da APC ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko wani wakili kan sauya sheka ba.

“Muna fayyacewa, ba tare da wata rudani ba, cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai taba shiga tattaunawa ko ganawa da APC kan sauya sheka ba. Wadannan ikirari karairayi ne marasa tushe,” in ji shi.

Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ake yawan yada jita-jita cewa Kwankwaso ya gabatar da wasu bukatu domin sauya sheka, tana mai gargadin cewa irin wadannan labarai na iya yaudara da kuma lalata suna.

Ta yi kira ga ’yan jarida da kafafen yada labarai su tsaya kan gaskiya da sahihan tushe, ba kan jita-jita ko maganganun siyasa ba.

Kwankwasiyya ta ce ganawar karshe tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu ta gudana ne a watan Janairu 2024, kuma babu wata tattaunawa kan sauya sheka ko yarjejeniya ta siyasa a lokacin.

Sanarwar ta bayyana cewa rahotannin da ake yadawa wani shiri ne na wasu ’yan siyasa domin rage karfin Kwankwaso, tare da nuna cewa yawancin masu yada labarin sun riga sun sauya sheka zuwa APC, don haka suna neman kare matakinsu da labarai marasa tushe.

Kungiyar ta jaddada matsayin Kwankwaso a matsayin dan siyasa mai ka’ida da tsari, wanda karfinsa ke fitowa daga talakawa ba daga yarjejeniyar manya ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *